Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu..
Wannan dandalin mun samar da shi ne da nufin taimakawa ƴan uwa musamman masu amfani da harshen Hausa wurin kawo bayanai da kuma taimako akan guraben karatu kyauta wato FULLY FUNDED SCHORLASHIP/منحة كاملة a ƙasar Saudiyya da ma sauran ƙasashe.
Amma a sauran ƙasashen zamu dinga kawo Schorlaships na Islamic studies ba lallai mu kawo na boko ba.
----------------------------------
Za muyi ƙoƙari duk lokacin da aka buɗe Schorlaships mu kawo ta da kuma gamsasshshen bayanai kan yadda ake cike ta da kuma requirements ɗinda ake buƙata.
Schorlaships ɗin Saudi za muyi ƙoƙarin yin screen vedio ta yadda kowa zai iya kallo yayi applying da Kan shi,a huta da biyan application fee.
Wanda ke da ƙarancin fahimta kar yayi gaggawar cikewa,ya ba wani ya cike masa ko ya tsaya har ya tabbatar da ya iya,gudun kar yayi kuskuren da zai sa ayi rejecting ɗin application ɗin shi.
_______________________
Za mu dinga kawo online courses/دورات العلمية عن بعد domin samun ilimi da kuma certificates waƴanda za mu yi amfani da su wurin neman Scholarships,kuma suna ƙarawa yiwuwar samun Addmision ɗin mutum ƙarfi,(wato suna ƙara possibility na acceptance)
Akwai waƴanda sai anyi jarrabawa ake samun certificates akwai kuma wa'yanda ba sai anyi jarrabawa ba.
_________________________
Za muyi ƙoƙari wurin binciko abubuwan da ko wace Schorlaship ta ƙunsa(what the Schorlaship covered),kama daga visa, Tickets,wurin zama,abinci da sauran su.
-----------------------------------
Schorlaship ta Saudiyya ana buƙatar documents da ɗan yawa ciki Hadda translation ɗin documents,to za mu yi ƙoƙarin sādā ku da masu tarjama(certified Translators)waƴanda muka yadda da Ingancin aikin su,sauƙin shi da kuma cika alqawarin su..
.........................................
Ni a matsayi na na wanda ke tafiyar da wannan platform ba zan yi alaqar kuɗi kai tsaye da kowa ba,kuma ba zan wakilta wani yayi alaqar kuɗi da kowa ba,in banda masu translation Suma zan haɗa ku ne in ba kada wanda zai yi maka,sai ku daidaita tsakanin ku,zan yi ƙoƙarin haɗa ku da masu adalci
.......................................
Documents ɗin da ake buƙata wurin applying Schorlaship na Saudi hya su kamar haka, da kuma inda ake samun ko wane yadda doka ta tanada(legally).
A guji yin takardun bogi saboda suna jawo matsala koda mutun ya je can ne.
----------------------------------
1. High school Certificates. WAEC, NECO,NBAIS da sauran su.wannan kowa yasan inda ake samun su..
2. Transcript. Ana samun ta a makarantar da ka gama Secondary
3. Testimonial. A makarantar da ka yi Secondary
4. International passport. A ofishin immigration
5. Police Clearance Certificate. A ofishin ƴan sanda
6. Certificate of medical Report. A Asibiti ake samun wannan.
7. Recommendation letters (Tazkiya) A wurin malamai musamman waƴanda suka yi karatu a Saudiyya
8. BIRTH certificate Amma ba dole ba ce
9. Personal passport mai background fari
10. Shedar haddace Alqur'ani.
11. Other Documents/شهادة إضافية irin wa'yannan da nayi alqawarin kama kawo inda ake samun su.
------------------------------------
Kar wanda ya samu wata takarda a ha yar da ba wannan ba,in ba haka ba za ka iya zuwa makaranta daga baya a maida ka gida..
-------------------------------------
Duk wani abu da nayi ko zan yi na yi for free fi sabilillah,ba wani aiki da zanyi dan abiya Ni,,burina duk mu cimma nasara.
--------------------------------------
A facebook wannan shine kaɗai Page ɗin mu..📌📌✍️✍️
________________________
A WhatsApp kuma muna da WhatsApp group da kuma Channel,
Ga su kamar haka
Group: https: https://chat.whatsapp.com/BuRHpVi1Vi83FRAaxeLTT6
Channel: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6L6Wu1SWsxf9BPYR1s
__________________________
A yi joining wa'yannan domin samun updates....
BURINA SHINE SAMAR MUKU DA FARIN CIKI.
والله المستعان
30/12/2025