WAYE SALMANUL FARISIY ?

Wannan labarin sahabi ne mai Neman gaskiya ako’ina take, salmanul farisiy yakawo labarin kansa da kansa, ga abinda yake cewa.

Ni matashi ne daga farisa daga mutanen Asbahan daga wata alqarya ana kiranta jayyana. Babana shine shugaban wannan alqarya, kuma yafi kowa dukiya a garin, kuma yafi kowa matsayi.

Ni babana yafi so fiyeda kowa tunda aka haifeni, haka son da yakemin yaci gaba da karuwa harsaida yatsare ni agida kamar yadda ake tsare yammata duk Dan kar wani Abu yasameni.

Mun kasance masu bautan wuta, muna zama mu yita ‘izata don karta mutu (majusawa) wata rana sai wani uzuri ya kama babana na tafiya cikin alqarya, sai yace min dana kaga uzuri ya taso min kaje yau ka jibinci mana al’amura.

Lokacin danake akan hanyan zuwa sai kuwa naci karo da coci na nasara sai naji muryoyinsu sunata sallah hakan sai yadauka hankalina.

Ni bansan komai akan addinai ba sai addinimmu na bautan wuta saboda kulleni da akeyi, sai kawai na yanke shawaran inshiga cocinnan inga abinda sukeyi.

Lokacin da naga yadda sukeyi nayi sha’awar addininsu nace wallahi wannan shine mafi alkhairi akan abinda muke akanshi. Ai acan na yada zango har rana ta fadi banje inda aka turani ba, saina tambayesu inane asalin wannan addinin naku?? Sai sukace a sham.

Lokacin da nadawo gida babana yaganni sai ya tambayeni akan inda ya aikani, sai nace lokacin ina kan hanya naga wasu mutane a cocinsu sunata sallah saina tsaya wurinsu harsaida rana tafadi, sai babana ya tsorata yace, Dana babu alkhairi acikin wannan addinin, addininka Dana ‘iyayenka yafi wannan!! Sai nace wallahi baba addininsu yafi namu alkhairi, sai babana yaji tsoron abinda nafada kar nayi ridda nabar addini na sai ya tsareni a gida yasamin mari a kafafuwana.

Lokacin da dama tasamu gareni saina aika wannan coci cewa in ansamu mai tafiya sham su sanar dani, sai kuwa aka bani labarin akwai mai zuwa dukda marin da aka samin saida nasan yadda nayi na gudu muka tafi tareda shi harsaida muka isa sham.

Lokacin da muka isa sham saina tambaya wane mutum ne yafi kowa acikin wannan addinin naku? Sai sukace usqufu mai kula da coci, sai kuwa naje wurinshi nace, ina sha’awan addinin nasara, inaso inzauna tareda kai, inyi maka hidima, inkoyi ilimi daga gareka indinga sallah tareda kai. Sai ya karbe ni nazauna wurinshi ina masa hidima.

Ban Dade tareda wannan mutum ba, nafahimci ba mutumin kirki bane, yana umurtan mutane da sadaqa ya kwadaitar dasu ladan da zasu samu amma idan suka kawo sadakar baya bama mabukata da miskinai sai yatara don kansa, harsaida yatara dinare mai uban yawa, nikuwa saina tsane shi nakama jin haushinsa saboda abinda nagani.

Ba’a Dade ba ya rasu, sai nasara suka taru don su birneshi, sai nace musu wannan mutumin mutumin banza ne yana umartanku da sadaka ya kwadaitar daku amma ‘idan kuka kawo sai yataskace don kansa, baya bawa masakai da faqirai.

Sai sukace ya akayi kasan haka!? Sai nace innuna muka taskanshi? Sukace eh, sai kuwa na nuna musu suka Ciro akwati bakwai cike da dinare da azurfa, da suka ga haka sai sukace wallahi bazamu birneshi ba, sai suka tsireshi suka jefeshi da duwatsu.

Ba’a Dade ba aka maye wanda ya mutun da wani, bantaba ganin mutum mai gudun duniya da kwadayin lahira kamarsa ba, jajirtacce ne a ‘ibada dare da rana, hakan yasa naso shi so wanda yabi jinina nazauna kuma tareda shi tsawon lokaci.

Lokacin da mutuwa yazo mashi sai nace mai, dawa kake min wasiyya in kasance abayanka!?

Yace Dana bansan wani mutum mai yin addinin nan da gaskiya ba irin yadda nakeyi wanda bai canza addininnan ba kuma bai juya shiba saidai wani mutum a mausil( msusil yankine acikin ‘Iraqi).

Lokacin daya rasu saina tafi wurin wannan mutumin a mausil na bashi labarina da wanda yaturo ni wurin sa, sai yace nazauna tareda shi, sai kuwa na sameshi mutum mai cikeda alkhairi.

Lokacin da yazo mutuwa sai nace dawa kake min wasiyya na kasance a bayanka!? Sai yace bansan wani mutum ba dayake kan gaskiya sai wani mutum daya a nasibin.

Lokacin da mutuwa ta dauki wannan din sai kuwa natafi wurin wannan din na nasibin, dana bashi labarina, sai yace kazauna tareda mu, sai kuwa na sameshi akan alkhairi kamar wadancan.

Ban Dade ba awurin shi shima sai mutuwa tazo masa, sai nace masa dawa kake mini wasiyya ? Kuma mai kakeso nayi abayanka? Sai yace wallahi Dana bansan wani mutum ba adoron kasa wanda yake akan addinin gaskiya wanda ba’a canza shi ba. Amma wani zamani yakusa da za’a aiko da wani annabi a yankin larabawa da yake akan addinin ibrahim, kuma zaiyi hijira daga garinsa zuwa wani gari mai yawan ‘itatuwan dabino a tsakanin duwatsu. Yanada wasu alamomi wadanda ba boyayyu bane sune……….

Yana cin kyauta amma baya cin sadaqa.

A tsakanin kafadunsa akwai tambari na annabta.

Idan kasamu daman zuwa wannan garin to kaje, sai mutuwa tazo ta daukeshi, saina zauna bayanshi agarin wani Dan lokaci sai wasu yankasuwa sukazo larabawa, sai nace musu idan kuka tafi dani tareda Ku zan Baku shanu na da dabbobi na. Sai suka yadda suka tafi dani lokacin da mukaje wadil qurrah (wani wuri ne tsakanin madina da sham amma yafi kusa da madina) sai suka yaudareni suka sayar dani ga wani mutum daga yahudu, sai nakoma mai yi masa hidima.

Ban Dade ba sai Dan amminsa ya ziyarce shi daga bani quraizhah sai yasiye ni awurinsa yatafi dani yasriba (madina) sai ko naga dabinon da aka siffata min, saina gane cewa nanne garin da akayi min kwatancensa.

Lokacin kuwa Manzon Allah yariga ya bayyana a maka amma ni banji labarinsa ba saboda shagaltuwa da ayyukan da ake doramin.

Ba’a Dade ba sai manzo s.a.w yayi hijira zuwa madina nikuma Ina karkashin wata bishiyar dabino inama shugabana aiki shima shugaban Nawa yana zaune awurin. sai Dan amminsa yazo yace masa, Allah ya halaka baniy qailata (AU’s kenan da kazraj) suna can sun taru a quba saboda wani mutum da zaizo musu daga Makkah yana cewa wai shi annabi ne.

Ai inajin labarin sa sai wani Abu naji ya kamani kamar zazzabi nayi sauri naje nakara tambayar mutumin mai kace!? Don Allah Dan kara bani labarin, sai shugabana yayi fushi mai tsanani yayi min wani kamu mai karfi yace, me ya shafeka da wannan!? Yace wuce koma kayi aikinka.

Yamma nayi na tattara wani dabino da nake dashi natafi inda naji ance manzo s.a.w yasauka, na shiga wurin sa nace, labari yazo min cewa kai mutumin kirki ne, kuma kanada sahabbai baki mabukata, nikuma inada wani dabino na sadaka sai naga Ku kuka fi cancanta dashi fiyeda wasunku.

Dana tafi naci gaba da Tara wani dabino, lokacin da manzo yabar kuba ya ‘iso madina sai nazo dashi nace, naga baka cin sadaka ga kyauta nazo in karramaka da ‘ita, sai yakarba yaci kuma ya umurci sahabbansa da suci suma tareda shi.

Sai kuwa nafada ‘araina alama ta biyu kenan, sai Nazo wurin Manzon Allah s.a.w a baqi’al garkad inda sukaje birni wani acikin sahabbansa, sai nayi musu sallama, na juya inata kallon bayansa ko zanga wannan tambari na annabta da shugabana ya siffanta min abaya. Manzo s.a.w kuwa yana daure da zani daya kuma ya yafa daya, lokacin da yaga ‘inata kallon bayansa sai yacire mayafinsa naga tambarin, sai nagane shi, naje na rungume shi ina kuka ina sumbantanshi.

Sai manzo s.a.w yace min meye labarin ka? Sai na bashi labari yayi mamaki, sai yace naba sahabbanshi labari na, saina basu, sukayi al’ajabi kuma sukayi farinciki mai tsanani.

Amincin Allah ya tabbata ga salmanul FARISIY mai Neman gaskiya ako’ina take, manzo s.a.w yace da imani wani abune mai wuyanci tabbas wani namiji daga cikin wadancan mazajen sai ya cishi yana nuna salman da hannunsa.

Amincin Allah ya tabbata ga salmanul FARISIY har ranar dazai tashi a gabanshi.

RADIYALLAHU ANHU.