Ƙamus turanci dictionary, kuma akan kira shi da suna littafin kalmomi, kundi ne na tarin kalmomi a Jere, a cikin harshe ko harsuna daban-daban, ana kuma jera kalmomin ne a tsarin zuwan baƙaƙe, ƙamus na dauke da bayanai na ma'anoni, anfani, etymologies, furucci, fassarori, na kalmomin dake cikin harshe da sauran su.[1] ko kuma ƙamus kan zama wani littafi ne dake ƙunshe da kalmomin dake cikin wata harshe da kuma irin su daga wata harshen, wanda ake kira da turanci lexicon.[1] It is a lexicographical reference that shows inter-relationships among the data.[2]

Akwai babban muhimmin banbanci da akayi tsakanin ƙamus na gama gari wanda ake kira da general da kuma ƙamus mai muhimmanci wato specialized dictionary. Shi ƙamus mai muhimmanci yana ɗauke ne da kalmomi da suka keɓanci wani fanni na ilimi kawai, bawai yana ɗauke da dukkanin kalmomin harshe bane. Su kuma kalman da ake amfani da su wurin fayyace kowane ma'ana na kalmomin ana kiran sune da suna terms bawai kalmomi ba wato words.[3] Har wayau akwai wasu nau'ukan ƙamus, waɗanda ke da tsarin su daban, misali, ƙamus mai harsuna biyu bilingual (translation) dictionary, ƙamus mai bada ma'anoni iri ɗaya dictionary of synonym (thesaurus), da kuma ƙamus da ake kira rhyming dictionary da turanci.[4]




Kamus Na Turanci Da Hausa Download